
A yau Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage yanke hukunci a karar da ta shigar da ke neman tsige Dr Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa zuwa ranar 23 ga watan Satumba.
Zaman hukuncin, wanda tun da farko aka saka za a yi shi a yau, ba ya cikin jerin kararrakkn da aka ambata a yau.
NAN ta tattaro cewa tun da fari, magatakardar kotun ya tuntubi masu kara da wadanda ake kara domin a dage ranar da za a yanke hukunci saboda hukuncin bai kammala ba.
“Mun kira bangarorin biyu ta wayar tarho domin sanar da su halin da ake ciki. Sabon kwanan wata shine mako mai zuwa, Satumba 23, ”in ji wata majiya mai tushe.
Tun a ranar 5 ga watan Yuli, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya sanya yau a matsayin ranar yanke hukunci.
Masu shigar da karar sun bukaci kotun da ta hana Ganduje ci gaba da bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar APC.
Mai kara; Kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya, karkashin jagorancin Saleh Zazzaga ce ta shigar da karar ne domin neman bahasi kan halascin nadin Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC alhalin shi ba dan shiyyar Arewa ta tsakiya ba ne.
A cikin karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/599/2024, mai shigar da karar ya bayyana Ganduje da APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a matsayin wadanda ake kara na 1 zuwa 3.