Home Labarai Kotu ta aika ɗan shekara 37 gidan yari sakamakon satar maggi

Kotu ta aika ɗan shekara 37 gidan yari sakamakon satar maggi

0
Kotu ta aika ɗan shekara 37 gidan yari sakamakon satar maggi

 

 

Kotun Shari’ar MuslunciMuslunci ta aike da wai mutum mai suna Yusha’u Ado zuwa gidan yari bisa zargin satar katan 22 na maggi.

A yau ne a ka gurfanar da Ado a gaban kotun bisa laifuka biyu da su ka haɗa da cin amana da kuma cuta, inda ya kuma amsa laifukan bayan an karanto masa su.

Ɗan sanda mai ƙara, Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa wani mai suna Jamilu Ibrahim, mazaunin unguwar Galandanci ne ya kawo korafin a caji-ofis na Sabon Gari a ranar 10 ga watan Maris.

Rubutaccen bayanan ƙarar ya ce Ibrahim ya baiwa Ado ajiyar kayan ɗin maggi 260 ya ajiye masa, amma da ya zo karba, sai gano cewa babu kwalaye 22 na maggin, wanda kuɗin sa ya kai naira dubu 261.

Bayan ya gama jin karar, alkalin kotun, Dakta Bello Khalid, ya bada umarnin mayar da mai laifin gidan yari sannan ya dage sauraron ƙarar zuwa ranar 8 ga watan Afrilu.