Home Labarai Kotu ta aike da ɓarawon kare gidan gyaran hali a Kano

Kotu ta aike da ɓarawon kare gidan gyaran hali a Kano

0
Kotu ta aike da ɓarawon kare gidan gyaran hali a Kano
A roaming dog roams around the village

 

Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Fagge a Jihar Kano ta aike da wani matashi zuwa gidan gyaran hali bayan ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa na satar kare.

Matashin, mai suna Alhassan Yusuf, mai kimanin shekara 21 dai ya amsa aikata laifin satar karen wanda darajarsa ta kai kusan Naira 10,000.

Alhassan dai mazaunin unguwar Tudun Maliki ne da ke Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa a na tuhumar matashin ne da laifuffuka guda biyu da suka jiɓanci ketare iyaka da kuma sata.

Tuni dai ya amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawar.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Bello Khalid, ya umarci a tsare wanda ake tuhumar a gidan gyaran hali, sannan ya dage ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa ranar uku ga watan Disamba domin yanke hukunci.