Home Labarai Kotu ta aike da babban ɗan adawar Ganduje, Muaz Magaji gidan yari

Kotu ta aike da babban ɗan adawar Ganduje, Muaz Magaji gidan yari

0
Kotu ta aike da babban ɗan adawar Ganduje, Muaz Magaji gidan yari

 

Kotun Majistare mai lamba 58 da ke zaman ta a unguwar Nomansland ta aike da tsohon Kwamishinan Aiyuka da Gine-gine na Jihar Kano, Muaz Magaji zuwa gidan yari.

Kotun na tuhumar Magaji, wanda fitaccen ɗan adawar Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da kaifuka huɗu.

Laifukan sun haɗa da ɓata suna, cin mutunci da gangan, ƙarya da nufin zubar da kima da kuma ta da hankali, laifukan da su ka saɓa da sashe na 392, 399 da 114 na kundin dokar Kano ta 1999.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa bayan da a ka karantowa Magaji laifukan, sai ya musanta dukkan su.

Daga bisani sai lauyan Magaji, Gazzali Ahmad ya roƙi kotu da ta bada belin wanda a ke ƙara sakamakon bashi da lafiya.

Sai lauyan mai ƙara, W. A. Wada ya yi suka a kan bada belin wanda a ke ƙara sakamakon rashin 2ata kwakkwarar hujja da ta nuna cewa wanda a ke ƙara yana cikin rashin lafiya mai tsanani da har za ta isa a zaman hujja ta bada belin sa.

Da ga ƙarshe ne dai alƙalin kotun, Aminu Gabari, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 3 ga watan Febrairu domin yanke hukunci a kan yiwuwar bada belin na Magaji, wanda a ka fi sani da Ɗan Sarauniya.

Da ga bisani, da ya ke yanke ƙwarya-ƙwaryan hukunci, alƙali Gabari ya bada umarnin a aike da Magaji gidan yari har sai ranar 3 ga watan Febrairu.