
Wata Kotun Shari’a da ke zaman ta a Rigasa, Jihar Kaduna ta aike da wasu kishiyoyi matan wani mutum mai suna Danlami Tasiu zuwa gidan yari na tsawon mako biyu sakamakon faɗa da cizon juna da su ka yi a unguwar Bukuru da ke jihar.
Alkalin kotun, Salisu Abubakar-Tureta ya yanke hukuncin ne bayan da ya gano cewa duka matan biyun ne su ka doki juna ba kamar yadda ɗaya ta faɗawa kotu cewa ita a ke duka da ƙuntatawa ba.
Tureta ya ce aikewa da su gidan yarin wani mataki ne na ladabtar da su domin su canja halayen su.
Ya kuma ɗage ci gaba da shari’ar zuwa 28 ga watan Fabrairu.
Ɗaya da ga cikin matan, Azima Usman Tasiu ce ta kai ƙarar kishiyarta Aisha Tasiu kotu cewa ta doke ta da kuma cizon ta.
Azima ta shaidawa kotun cewa ita ce matar Tasiu ta uku kuma sun samu matsala da Aishar ne a kan ɗan ta.
Ta ƙara da cewa ranar girkinta ce, ta je ta ɗebo ruwa a rijiya, sai ta tar da shi ɗan gidan kishiyarta, Aisha a wajen, shi kuma sai ya ƙi ya bata waje ta ɗibi ruwan, shi ne sai mahaifiyar ta sa ta zo ta dauke gugar ɗiban ruwan ta kai ta ɗaki.
“Da na bita na karɓi gugar shine ta mare ni, ta riƙa duka na har da cizo,” in ji Azima.
A nata ɓangaren, Aisha, wacce ita ce matar Tasiu ta biyu, ta ce Azima ce ta fara dukan ta, in da ta biyo ta a baya 5a dake ta sannan ta cije ta a kafada.
Da ga nan alƙalin, domin ya yi adalci tsakanin su, sai ya ce ko wacce ta nuna inda a ka cije ta, su ka kuma nuna ɗin.
Sai ya ƙara da cewa lamarin na mutum biyu ne da su ke faɗa da juna, ba wai ɗaya ce ta ci zalin ɗaya ba.
Haka shi ma Tasiu ya ce da ya shiga gidan ya same su su na faɗa kuma ya yi ƙoƙarin ya raba su amma su ka ƙi rabuwa.
Tasiu ya kuma ƙara da cewa ko ka dai wanne hukunci kotun ta yanke a ranar 28 ga watan Fabrairu ɗin, to zai yi wuya idan bai saki su biyun ba.