Home Labarai Kotu ta aika matasa 2 gidan yari bisa garkuwa da kashe wani yaro bayan karɓar kuɗin fansa

Kotu ta aika matasa 2 gidan yari bisa garkuwa da kashe wani yaro bayan karɓar kuɗin fansa

0
Kotu ta aika matasa 2 gidan yari bisa garkuwa da kashe wani yaro bayan karɓar kuɗin fansa

 

Kotun majistare mai lamba 60, karkashin mai Shari’a Tijjani Saleh Minjibir a jihar Kano ta aike da wasu matasa su biyu zuwa gidan yari bisa zargin yin garkuwa da wani yaro.

Kotun dai na tuhumar Dalha Gambo, mazaunin garin Halambe da Hannafi Hassaan, mazaunin garin Iyaye, duk a Ƙaramar Hukumar Ningi a jihar Bauchi da laifin hada baki da garkuwa da wani yaro mai suna Muhammad Tasi, ɗan Karamar Hukumar Sumaila a jihar Kano.

Bayan sun yi garkuwa da yaron, sai su ka nemi kuɗin fansa Naira dubu 705 kuma a ka biya su.

Bayan sun karɓe kuɗin fansar, sai kuma su ka jefa shi cikin rijiya ya rasu a ciki.

Sai dai kuma waɗanda ake zargin sun musanta tuhumar da ake musu.

Mai Shari’a Minjibir ya bada umarnin aike wa da su gidan yarin zuwa ranar 9 ga watan Janairun 2023 domin sake gurfanar da su.