Home Labarai Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar gwamnatin Nijeriya ta maida shari’ar Abba Kyari zuwa Amurka

Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar gwamnatin Nijeriya ta maida shari’ar Abba Kyari zuwa Amurka

0
Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar gwamnatin Nijeriya ta maida shari’ar Abba Kyari zuwa Amurka

 

 

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta yi watsi da ƙarar da gwamnatin ƙasar ta shigar ta shigar ta neman a tisa ƙeyar Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ɗan sandan da aka dakatar saboda zarginsa da ta’amali da hodar iblis zuwa Amurka.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi fatali da ƙarar da Ministan shari’a, Abubakar Malami, ya shigar bisa dalilin cewa ƙarar na da naƙasu.

A watan Yulin 2021 ne rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta dakatar da DCP Abba Kyari bisa zargin karɓar cin hanci daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppid – mutumin da ke tsare a Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin dala.

Hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya, NDLEA ta ce kamen da aka yi da yawan mutanen da aka tsare a cikin wata 12 da suka gabata alama ce da ke nuna cewa a baya an raina girman matsalar tu’ammali da miyagun ƙwayoyi da ƙasar ke ciki, kafin Shugaba Buhari ya ƙarfafa hukumar NDLEA.