
A jiya Laraba ne wata kotu da ke Ikeja da ta yanke wa Ayodeji Oluokun, mataimakin limamin cocin Redeem Christian Church of God, RCCG, City of David Parish da ke unguwar Victoria Island, Legas, hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari bisa samunsa da laifin bayar da chek na kuɗi har na dala miliyan 1.6 amma na bogi.
An gurfanar da Oluokun ne tare da kamfaninsa, Peak Petroleum Industry Nigeria Ltd., a kan wasu tuhume-tuhume shida da aka yi wa kwaskwarima da suka hada da bayar da cek, sata da kuma karɓar kudi bisa ƙarya.
Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo, a hukuncin da ya yanke, ta ce masu gabatar da ƙara sun samu nasarar tabbatar da gaskiyar tuhumar da ake yi wa wanda a ke ƙara na bada cek na ƙarya.
Sai dai Taiwo, ya sallami wadanda ake tuhuma da laifin sata da kuma samun kuɗi a bisa zargin karya.
“Wanda ake tuhumar ya bayar da cek guda biyu a cikin kudi dala miliyan 1.6 ga wanda ya shigar da kara, wanda hakan rashin girmamawa ne saboda babu kudi a asusun wanda ake karar.
“Bayar da cek alhali babu kuɗi a asusu babban laifi ne.
“Idan da gaske ne wanda ake tuhuma yana jiran wasu kudi har zuwa karshen watan Yulin 2014 kamar yadda ya yi iƙirari, da ya jira har sai ya karɓi kuɗin kafin ya ba da cek ɗin a ranar 24 ga Yuni, 2014,” in ji Taiwo.