Home Labarai Kotu ta bada belin Muaz Magaji

Kotu ta bada belin Muaz Magaji

0
Kotu ta bada belin Muaz Magaji

 

Kotun Majistare a Jihar Kano ta bada belin tsohon Kwamishinan Aiyuka da Gine-gine, Muaz Magaji.

Kotun na tuhumar Magaji, wanda fitaccen ɗan adawar Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ne da kaifuka huɗu.

Laifukan sun haɗa da ɓata suna, cin mutunci da gangan, ƙarya da nufin zubar da kima da kuma ta da hankali, laifukan da su ka saɓa da sashe na 392, 399 da 114 na kundin dokar Kano ta 1999, amma kuma ya musanta duka laifukan.

Da ya ke ƙwarya-ƙwaryan hukunci a kan bukatar da lauyan wanda a ke ƙara ya miƙa masa ta neman beli, alƙalin kotun, Majistire Aminu Gabari, ya amince da roƙon ya kuma bada belin wanda a ke ƙara.

Sharuɗɗan belin sun haɗa da naira miliyan 1 da kuma waɗanda za su tsaya masa mutum biyu.

A cikin mutum biyun da za su tsaya masa, in ji alƙalin, a kwai Dagacin ƙauyen Ɗan-Sarauniya, sai kuma Kwamnadan Hisbah na Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ko kuma Babban Limamin Ƙaramar Hukumar.

Hakazalika kotun ta bukaci Magaji da ya kai mata fasfo ɗin shi na tafiye-tafiye, inda su ma mutum biyun da za su tsaya masa sai sun kai hotunan su.

Sannan kotun za ta tura ma’aikatan ta su duba gidajen mutum biyun da za su tsayawa Magaji.

Sai alƙalin ya ɗage sake zaman shari’ar sai ranar 2 ga watan Maris.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa bayan an gama zaman shari’ar, sai ma’aikatan gidan gyaran hali su ka saka shi a mota su ka maida shi gidan gyaran hali har sai ya cika sharuɗɗan belin.