Home Labarai Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano da ga gina shaguna a Kasuwar Wambai

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano da ga gina shaguna a Kasuwar Wambai

0
Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano da ga gina shaguna a Kasuwar Wambai

 

Wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta dakatar da Gwamnatin jihar da ga gina shaguna a tsakiyar Kasuwa Wambai a Ƙaramar Hukumar Municipal.

Tun da fari, ƴan kasuwar su ka yi bore kan ginin shagunan bayan da gwamnati ta fara aza tubalin ginin.

Ƴan kasuwar sun koka cewa idan a ka gina shagunan, to zai kassara cinikaiyar su saboda layin da gwamnatin za ta gine, shine babban layi da motoci su ke tsayawa su yi lodin kaya zuwa wasu sassa na ƙasar nan.

Ganin cewa gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu da duk koken da su ke yi na kar ta yi ginin, sai ƴan kasuwar su ka garzaya kotu domin a bi musu haƙƙin su.

Da ta ke sauraron ƙarar da ƴan kasuwar su ka shigar a yau Juma’a, Alƙaliyar kotun, A’isha Ya’u ta baiwa gwamnatin umarnin ta dakata da ginin har sai an saurari dukkan bangarorin biyu.

Ta kuma umarci dukkan bangarorin biyu da su dakata da ɗaukar wata matsaya a kan ginin.

Kotu ta ɗauki wannan mataki ne tun bayan karɓar ƙorafin da ta yi a ranar 17 ga watan Disamba.

Alkaliyar ta ɗage jin sauraron ƙarar zuwa 24 ga watan Janairu, 2022.