
Wata Babbar Kotun Taraiya da ke zaman ta a Kano ta dakatar da shugabancin jam’iyar PDP, ƙarƙashin Shehu Sagagi har sai ta gama sauraron ƙarar da a ka shigar a gaban ta.
Ana zargin Sagagi da biyayya ga tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Kwankwaso.
Wani Bello Bichi ne ya shigar da ƙarar a gaban Mai Shari’a A. M. Bichi, inda ya yi ƙarar PDP, INEC da sauran mutane 40.
Kotun ta ce ta bada umarnin ne domin gujewa wani yanayi da za a zama babu shugabci a jam’iyar, shi ya sanya ta bada umarnin ga wanda a ke ƙara na 3 har zuwa na 42.