
A yau Alhamis ne kotun majistire ta bada umarnin ci gaba da ajiye wani malamin makaranta, Sukairaj Kabir, mai shakara 38 a gidan yari a bisa zargin yi wa ɗalibarsa mai taɓin hankali, ƴar shekara 15 fyaɗe.
Kabir, wanda ya ke zaune a Rimin Auzinawa a Kano ya musanta tuhumomi biyu da a ke yi masa na yiwa yarinya fyaɗe.
Alƙalin kotun, Mustapha Sa’ad-Datti ya bada umarnin a ci gaba da tsare wanda a ke zargin a gidan yari, sai ya daga sauraren ƙarar zuwa 10 ga watan Janairu, 2022.
Tun da fari, lauya mai ƙara, Asma’u Ado ta sahidawa kotun cewa wanda a ke ƙara ya aikata lefin ne tsakanin 2018 da 2021 a unguwar Tudun Yola a Kano.
Ta ce wanda a ke ƙarar, kasancewar sa malamin makarantar su yarinyar, sai ya riƙa jan ta wani aji a makarantar da ke unguwar Tudun Yola.
“Ha ka wanda ake zargin ya riƙa yi mata fyaɗe har tsawon shekaru 4 tun lokacin tana ƴar shekara 12”, a cewar Ado.
Ta ce laifin ya saɓa da sashi na 283 da 238 ma kundin laifuka na Kano.