Home Siyasa Kotu ta hana PDP rushe shugabannin jam’iyar na Kano

Kotu ta hana PDP rushe shugabannin jam’iyar na Kano

0
Kotu ta hana PDP rushe shugabannin jam’iyar na Kano

 

Wata Babbar Kotun Taraiya a Abuja ta haramta wa uwar jam’iyyar PDP ta ƙasa rushe shugabannin jam’iyyar PDP na Jihar Kano.

A ƙwarya-ƙwaryar hukuncin da Mai Shari’a Taiwo O. Taiwo ya yanke a yau Talata, ya gargaɗi uwar jam’iyyar ta PDP da cewa ta bar shugabannin jam’iyyar na jihar kano da na Kananan Hukumomi da Kuma na Mazaɓu su cigaba da tafiyar da al’amuran jam’iyyar har lokacin da zata kammala sauraron shari’ar.

Mutane hudu ne suka shigar da karar ciki har da Shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Shehu Wada Sagagi da Bashir Shehu Muhammad, Ali Tijjani Ansaru, sai kuma Gambo Jamil Abba, Inda suke karar uwar jam’iyyar PDP ta kasa da Hukumar zabe mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC.

Itan ba’a manta ba dai tun lokacin da tsohon Gwamnan Jihar Kano Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya fara yunkurin fice da ga jam’iyyar ba tare da shugabannin jam’iyyar ba, ake ganin kamar shi ne ya hana su fita saboda wata manufa da yake so ya cimma, Kan tasa uwar jam’iyyar take kokarin rushe su.