Home Labarai Kotu a Jos ta daure wani dan kasuwa shekaru 2 bisa laifin yiwa yarinya fyade

Kotu a Jos ta daure wani dan kasuwa shekaru 2 bisa laifin yiwa yarinya fyade

0
Kotu a Jos ta daure wani dan kasuwa shekaru 2 bisa laifin yiwa yarinya fyade

Wata babbar kotun yanki dake Kasuwan Nama a garin Jos, a ranar Talata ta daure wani matashin dan kasuwa mai shekaru 25, mai suna Isiaka Rabiu daurin shekara biyu a gidan maza sabida kama shi da laifin yiwa yarinya ‘yar shekara 6 fyade.

Mai Shari’ah, Yahaya Mohammed, ya yankewa matashin hukuncin ne bayan da ya amsa laifinsa ba tare da gardama ba, inda kuma ya roki kotu da ta yi masa sassauci.

Alkalin ya daure mai laifin ne ba tare da bashi wani zabin tara ba, ya bayyana cewar wannan daurin zai zamar masa darasi kan laifin da ya aikata, domin kaucewa yin makamancinsa anan gaba.

Tun farko dai, dan sanda mai gabatar da kara, Ibrahim Gokwat, ya shaidawa kotu cewar, an kawo musu rahoton abinda matashin ya aikatawa yarinyar ne a sashin binciken manyan laifuka a ranar 5 ga watan Maris.

A cewarsa, mutumin da ake zargi da aikata laifin, mazaunin Sabon layin Farin-Gada ne, a wannan ranar ta biyar ga watan Maris, ya yaudari yarinyar zuwa dakinsa, inda ya haike mata, bayan yarinyar ta dawo daga Makaranta.

Ya cigaba da cewar, matashin ya jiwa yarinyar wasu raunuka a matancinta. Inda yace matashin ya aikata laifin da ya saba da kashi na 285 na kundin dokar final kod.

NAN