Home Labarai Kotu a Kano ta ƙi amincewa da buƙatar mayar da shari’ar Sheikh Abduljabbar Abuja

Kotu a Kano ta ƙi amincewa da buƙatar mayar da shari’ar Sheikh Abduljabbar Abuja

0
Kotu a Kano ta ƙi amincewa da buƙatar mayar da shari’ar Sheikh Abduljabbar Abuja

 

 

 

 

Wata kotun tarayya da ke zamanta a Kano, ta ƙi amincewa da buƙatar mayar da shari’ar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara zuwa babban birnin kasar Abuja.

Abduljabbar dai ya bukaci kotun da ta mayar da shari’ar tasa zuwa wata kotun a Abuja saboda zargin da yake na cewar kotun Kano ba za ta yi masa adalci ba.

A yayin zaman kotun na yau wanda ya gudana ƙarƙashin Mai Shari’a Abdullahi Liman, lauyan Abduljabbar Nasir Kabara Barista Dalhatu Shehu Usman ya zargi alkalin kotun tarayyar ta Kano da ganawa da kwamsihinan shari’a na Kano Barista Musa Lawan a safiyar yau gabanin zaman kotun.

Wanda ya ce bisa ƙa’ida bai kamata a ce alkalin ya yi hakan ba, wanda kuma hakan yasa Sheikh Kabara ya karaya da cewar ba zai sami adalci daga kotun ba.

Sai dai a wani martani da lauya gwamnati Barista Dahiru Muhammad, ya ƙalubalanci wannan batu.

Ya sanar da kotun cewar tun karfe 9 na safiyar yau, masu gabatar da ƙarar suka ba shi kwafin wata sabuwar ƙarar da suka shigar a Abuja na zargin take masa hakkinsa na dan adam, bayan batun na gaban alkalin wata kotu ta daban.

Daga nan ne sai Mai Shari’a Abdullahi Liman ya ce ba zai rufe shari’ar ba, sannan a shari’ance babu inda ake ce ɓangare daya da ake shari’a da shi zai ce lallai shi ga kotun da yake buƙata da ta saurari wata shari’ar.

Sannan ya umarci lauyan Malam Abduljabbar da ya rubuto zargin da yake yi kan zuwan Kwamishinan Shari’a na jihar Kano wajen sa, tare da tabbatar da abin da suka tattauna na da alaƙa da shari’ar da Abduljababr din ya shigar gabansa.

BBC Hausa ta rawaito a ranar 21 ga watan Yulin da muke ciki ne Shiekh Abduljabbar Nasir Kabara ya garzaya kotun tarayyar d ke Kanon, da bukatar a mayar da shari’ar da ake yi masa ta zargin ɓatancin ga Annabi SAW zuwa ga wani alkalin na daban.

Ya yi hakan ne saboda zargin cewar gwamantin Kano da Babbar Kotun Musulunci ta Kofar Kudu na take masa hakkinsa dan ɗan Adam.