
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a yau Talata ta baiyana cewa korar Sarki Sanusi ko zuwa Jihar Nassarawa bayan an tsige shi daga sarautar Kano ya saɓawa dokar ƙasa.
Alƙalin kotun, Anwuli Chikere, a hukuncin da ya yi a yau Talata, ya baiyana cewa Dokar Kafa Masarautar Kano ta 2019 da gwamnatin jiha ta kafa ta kuka yi amfani da ita wajen korar Sarki Sanusi bayan ta tsige shi ta saɓawa kundin tsarin mulki na 1999.
Ya ce kundin tsarin mulkin ƙasar nan shine a gaba kuma duk wata doka da a ka ƙir-ƙire ta ba abinda doron kudin ba to ba abar karɓa ba ce.
Alƙalin ya ƙara da cewa tsohon sarkin na Kano yana da ƴancin da zai zauna a ko ina a faɗin ƙasar nan har da ma Jihar Kano.
Kanfanin Daillancin Labarai, NAN ya rawaito cewa bayan da a ka tsige Sarkin a ranar 9 ga watan Maris, 2020, sai ya kai ƙarar Shugaban Ƴan Sanda na Ƙasa, Shugaban DSS na ƙasa a ranar 12 ga watan Maris, 2020 inda ya ke ƙalubalantarsu a kan cewa an tsare shi ba bisa haƙƙin sa ba.
Haka kuma a cikin waɗan da ya kai ƙarar har da Antoni-Janar na jiha da na ƙasa.
Saboda haka alƙalin ya umarci masu ƙara na 1 da na 2 da 3 su biya Sarkin Naira miliyan 10 da kuma bashi haƙuri ta kafafen yaɗa labarai.
Da ya ke martani a kan wannan hukuncin, Antoni-Janar na Jihar Kano, Mohammed Lawan ya baiyana cewa sun ji hukuncin kuma za su yi nazari a kai.
Da ya ke ganawa da manema labarai, Lawan ya ce gwamnatin jiha ta yi daidai da ta tsige Sarki Sanusi saboda ya sa ƙafa ya rushe al’adar masarautar Kano.