Home Labarai Kotu ta kori ƙarar da gwamnonin jiha su ka kai gwamnatin taraiya kan $418m na Paris Club

Kotu ta kori ƙarar da gwamnonin jiha su ka kai gwamnatin taraiya kan $418m na Paris Club

0
Kotu ta kori ƙarar da gwamnonin jiha su ka kai gwamnatin taraiya kan $418m na Paris Club

 

Wata Babbar Kotun Taraiya da ke Abuja, a jiya Juma’a ta kori ƙarar da gwamnonin jihohi 36 na ƙasar nan su ka shigar a kan Gwamnatin Taraiya kan bashin dala miliyan 480 na Paris Club.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya kori ƙarar ne kan dalilin cewa ba ta da tushe ballantana makama.

Ekwo ya ce masu ƙarar, da su ka haɗa da Antoni-Antoni Janar na jihohi, da Akanta-Akanta Janar na jihohi basu da ikon shigar da ƙarar, mai lamba FHC/ABJ/CS/1313/2021 ba tare da yardar gwamnonin su ba.

Ya ce ba su da ikon shigar da ƙarar, duba da sashi na 211 na kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999.

“Antoni-Antoni Janar na jihohi ba su da ikon yin gaban kansu su shigar da wannan ƙara.

“Ba wani mataki da za a iya ɗauka idan mai ƙara bashi da ikon shigar da ƙara a bisa doka,” in ji shi.

Ekwo ya ƙara da cewa ƙarar ba ta cikin irin ajin ƙararrakin da Antoni-Antoni Janar na jihohi za su shigar ba tare da amincewar gwamnonin su ba.