Home Siyasa Kotu ta rushe shugabancin APC na Abdullahi Abbas a Kano

Kotu ta rushe shugabancin APC na Abdullahi Abbas a Kano

0
Kotu ta rushe shugabancin APC na Abdullahi Abbas a Kano

 

Wata kotun tarayya dake Abuja, a ƙarƙashin jagorancin Hamza Muazu ta rushe zaɓen shugabancin jam’iyar APC da tsagin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya gudanar.

Haka kuma mai shari’ar ya tabbatar da zaɓen da tsagin tshohon gwamnan Kano Ibrahim shekarau ya gudanar.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewar mai shari’ar ya ce zaɓen na ɓangaren Shekarau, wanda Haruna Ɗanzago ya lashe, ya samu sanya hannun mutum 7 daga cikin waɗanda uwar jam’iyyar ta turo jihar Kano domin gudanar da zaɓen.

Alkalin kotun, Mai shari’a Hamza Muazu yace ya amince da zaben da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau suka gudanar.

Alkalin ya yanke hukuncin cewa bangaren Shekarau mai taken G-7 ya gudanar da zaben wanda kwamitin mutane 7 na APC ya sanya wa hannu.

Jaridar ta ruwaito cewa waɗanda su ka shigar da ƙara sun haɗa da Muntaka Bala Sulaiman da mambobin jam’iyyar 17,980, yayin da waɗanda a ke ƙarar su ne APC, a matsayin wanda ake kara na ɗaya, Mai Mala Buni, shugaban rio, Sen. John Akpanudoedehe sakataren jam’iyyar na ƙasa da kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.

Kotun ta ce duk taron da ɓangaren Ibrahim Shekarau ya jagoranta sahihine.

Nuraini Jimoh, SAN shi ne lauyan Masu Kara yayin da Sule Usman, SAN, M.N. Duru da Mashood Alabelewe Suka kasance Lauyoyin Waɗanda ake Kara.