
Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya da ke zamanta a Yenegoa, babban birnin Bayelsa ta yanke hukuncin cewa tsohon Shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan zai iya takarar shugabancin ƙasar
Rahotanni sun baiyana cewa alkali mai shari’a, Isa Hamma Dashen ne ya yanke wannnan hukunci a yau Juma’a.
Sai dai har zuwa yanzu Jonathan bai fitar da wata sanarwa ba da ke nuna cewa zai tsaya takara.
Ko a kwanakin baya sai da gamayyar kungiyoyi a arewacin Najeriya suka saya wa Jonathan fom ɗin takarar shugaban kasa, karkashin Jam’iyyar APC, duk da cewa Jonathan ɗin ya nesantar da kansa daga hakan.
Sai dai kuma da ga baya rahotanni su ka nuna cewa Jonathan ɗin ya amince da tsaya wa takarar shugabancin ƙasa.