Home Labarai Kotu ta saka matashi sharar titi mai tsawon kilomita 1 da bulala 12 a Kano

Kotu ta saka matashi sharar titi mai tsawon kilomita 1 da bulala 12 a Kano

0
Kotu ta saka matashi sharar titi mai tsawon kilomita 1 da bulala 12 a Kano

 

Wata Kotun Shari’ar Muslunci da ke zamanta a Rijiyar Lemo a Jihar Kano ta yi wa wani matashi, mai suna Usman Umar hukuncin gwale-gwale.

Alƙalin kotun, ya yanke wa matashin hukuncin ne bisa samun sa wuƙa da kuma kayan maye, mai suna sholisho.

Da ya ke yanke wa matashin hukunci, Alƙalin kotun, Abdu Abdullahi Waiya, ya ce ya dogara ne da sashi na 414 na kundin shari’a (penal code).

Ya ce laifin da a ka kama matashin da shi ya saɓawa tanadin sashin kundin shari’ar.

A hukuncin, Waiya ya umarci matashin da ya share titin Rijiyar Lemo zuwa unguwar Kurnar Asabe, tsawon kimanin kilomita ɗaya, inda zai kwashe mako ɗaya yana yin sharar.

Alƙalin ya kuma umarci matashin da ya share kwatar layin ƴan azara da ke unguwar Gwammaja, inda ya kuma umarci da a tsula masa bulala 12.domin a ladabatar da shi