
A yau Litinin ne wata Babbar Kotun Majistare da ke Kaduna ta bada umarnin sake tsare wani dan kasuwa mai suna Abdullahi Nurudeen mai shekaru 36 a gidan yari bisa zargin yin garkuwa da ɗan makwabcinsa.
Wanda ake zargin mazaunin titin Ali Akilu a Kaduna, ana tuhumarsa da laifuka biyu da suka hada da haɗa baki da kuma garkuwa da mutane.
Mai gabatar da ƙara, Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewa Farouq Sani na Sabon Gaya da ke Kaduna ya kai ƙoƙarin ne a caji-ofis na Gabasawa a ranar 9 ga watan Fabrairu.
A cewar mai gabatar da ƙara, a wannan rana da misalin karfe 4 na yamma, wanda ya shigar da ƙarar ya dawo daga aiki ya gano cewa yaronsa mai shekaru 10 da haihuwa ya ɓace.
Ya ce da mai ƙarar ya tambayi wasu maƙwabta ko sun ga ɗansa, sai aka ce masa an ga wanda ake ƙara da wasu mutane biyu da su ka tsere tare da yaron.
“Daga baya wanda ya shigar da karar ya kai kara wajen ‘yan sanda kuma tuni a kama wanda ake kara dangane da lamarin.
Leo, wani sifeton ƴan sanda ya kara da cewa, “A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake tuhumar ya amsa cewa ya hada baki da Aminu Hassan da Barau Ahmed da a yanzu sun gudu, don sace yaron.
Mai gabatar da kara ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 59 da 247 na dokar jihar Kaduna ta shekarar 2017.
Sai dai mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa an gabatar da lamarin a gabanta ne kawai domin ta sani, saboda kotun ba ta da hurumin sauraren karar.
Don haka Leo ya bukaci kotun da ta tasa keyar wanda ake kara domin ba da damar gurfanar da su a gaban kotun da ta dace.
Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara sannan ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 30 ga watan Mayu, domin baiwa ‘yan sanda damar mika takardar karar zuwa ga daraktan shigar da kara na jihar domin samun shawara.