
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ƙi amincewa da ba da belin dakataccen mataimakin kwamishinan ƴan sanda, Abba Kyari, da wasu mutum huɗu.
Da ya ke ƙwarya-ƙwaryan hukunci kan neman belin, Mai shari’a Emeka Nwite, ya ce waɗan ake zargin sun gaza gabatar da isassun kayayyaki da gamsassun hujjoji da zasu sanya Kotu ta amince da bukatar belin.
Bisa haka, Mai Shari’a Nwite, ya tabbatar da hukuncin farko da kotu ta yanke ranar 28 ga watan Maris, 2022 wanda ya umarci gaggauta shari’ar har a ƙare.