Home Labarai Kotu ta sanya ranar da za a gurfanar da Shugaban Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Ƙasa

Kotu ta sanya ranar da za a gurfanar da Shugaban Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Ƙasa

0
Kotu ta sanya ranar da za a gurfanar da Shugaban Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Ƙasa
A jiya Litinin ne Kotun Masana’antu ta Ƙasa da ke Abuja, ta sanya ranar 6 ga watan Afrilu domin sauraren ƙarar da a ka shigar a kan Shugaban Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Ƙasa, NUJ, Chris Isiguzo.
Mai shari’a Osatohanmwen Obaseki-Osaghae ya sanya ranar bayan da lauyan mai ƙara, Obinna Okeke ya buƙaci sanya wata ranar don fara sauraren ƙarar.
Tunda lauyan waɗanda a ke ƙara, Patrick Ediale, bai yi adawa da buƙatar ba, sai mai shari’a Obaseki-Osaghae ya sanya ranar 6 ga watan Afrilu domin fara sauraron ƙarar.
Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa Akindele Orimolade, Editan Jaridar New National Star Newspaper ne ya maka NUJ da Isiguzo a gaban kotu a matsayin waɗanda a ke tuhuma na 1 da na 2.
A cikin takardar sammaci mai lamba: NIC/ABJ/257/202,  mai ɗauke da kwanan wata 20 ga Satumba, 2021 da Okeke, lauya ga Orimolade, ya shigar a ranar 27 ga Satumba, 2021, lauyan ya yi roƙo ga kotu da ta baiyana cewa “bisa ga “Sashi na 3 (1) (a) (2) (b) na Kundin Tsarin Mulki na NUJ na Nuwamba 15, 2011, Isiguzo ba cikakken mamba ne a  NUJ ba.
Lauyan ya roƙi kotun da ta dawwamar da doka, tare da hana Isiguzo baiyana kansa a matsayin shugaban NUJ na ƙasa kuma ya daina shiga duk wata harka ta kungiyar gaba ɗaya, ta kowace hanya.
A cikin bayaninsa da ke tabbatar da dalilin daukar matakin, Orimolade ya bayyana Isiguzo a matsayin “dan jarida mai yaudara.”
A cewarsa, shi (Isiguzo) bai mallaki shaidar matakin karatu mafi kankanta da za ta bashi damar zama shugabancin kungiyar ba.
Ya ƙara da cewa Isiguzo bai cika wasu sharuɗɗa da kundin tsarin mulkin wanda ake ƙara na ɗaya ya bukata ba na sanya shi mamba na 1 da ake ƙara domin ya bashi damar tsayawa takara kuma a zaɓe shi a matsayin Shugaban ƙungiyar mai ci a zaben NUJ na kasa daga 4 zuwa 5 ga Oktoba, 2018.
Ya kara da cewa kafin zaben NUJ, Isiguzo ya shiga cikin badaƙalar shaidar karatu ta bogi, wanda har zuwa lokacin shigar da karar ba a wanke shi ba.