Home Labarai Kotu ta sassauta sharuɗɗan belin Danbilki Kwamanda

Kotu ta sassauta sharuɗɗan belin Danbilki Kwamanda

0
Kotu ta sassauta sharuɗɗan belin Danbilki Kwamanda

 

Kotun Majistare ta Jihar Kano mai lamba 58, karkashin jagorancin Aminu Gabari a yau Alhamis ta yi nazari kan sharuɗɗan belin da ta sanya wa Abdulmajid Danbilki Kwamanda.

Hakan ya faru ne sakamakon rokon da lauyan Kwamanda, Barista Tajuddeen Funsho ya yi a gaban kotun.

Da yake gabatar da roƙon, Funsho ya buƙaci kotun da ta sake duba sharuɗɗan da ta gindaya a baya a kan wanda yake karewa, inda ya ce wanda ake ƙara zai ci gaba da zuwa kotu domin sauraren laifukan da ake ƙarar sa a kai.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa laifukan da ake tuhumar Kwamandan da su sun haɗa da ɓata sunan gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

A martanin da ya mayar, lauyan masu shigar da kara, Barr. Wada Ahmad Wada, ya ce batun sake duba belin kotu ce ta yanke hukunci, inda ya yi fatan za a bi ka’idojin shari’a da adalci wajen sake nazarin.

A hukuncin da ya yanke, Alkalin kotun, Aminu Gabari, ya umarci Kwamanda da ya gabatar da mutane 2 wadanda su ka hada da: mahaifinsa ko wakilinsa, maimakon Wakilin Gabas na masarautar Kano da kotun ta nemi ya kawo da farko.

Hakazalika, kotun ta umarci wanda ake kara da ya gabatar da limamin duk wani masallaci da ke unguwar unguwar Ƙoƙi, ko kuma limamin kowane masallacin da ya ke gudanar da sallarsa a wajen.

Mai Shari’a Gabari ya kuma ba da umarnin cewa, haka nan wanda ake tuhuma zai iya kiran duk wani shugaban addini a cikin al’umma, idan har bai samu wani Iimami da zai tsaya masa ba.

Wannan ya maye gurbin Babban Limamin Masallacin Hajiya Mariya Sanusi Dantata da ke unguwar koki da kotun ta ambata a baya.

Kotun ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga Afrilu, 2023 don ci gaba da ambato.