
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta cire sunan Hamza Al-Mustapha a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Alliance (AA) a zaben 2023 mai zuwa.
Al-Mustapha ya lashe zaben fidda-gwani na jam’iyyar ne da kuri’u 506 inda ya doke Samson Odupitan wanda shi ne abokin karawar sa ɗaya tilo.
Manjo mai ritaya kuma tsohon mai taimaka wa marigayi Sani Abacha, an bayyana shi a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben fidda gwani na shugaban kasa na AA da aka gudanar a ranar 9 ga watan Yuni a Abuja.
A hukuncin da ta yanke a ranar Juma’a, alkali Zainab Abubakar, ta kuma umarci INEC da ta yi rangwame ga duk ƴan takarar da Kenneth Udeze, shugaban jam’iyyar ya mika mata.
An shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1759/2022 ne a ranar 30 ga watan Satumba ta hannun wani bangaren jam’iyyar, karkashin jagorancin Adekunle Omoaje.
Omoaje ya garzaya kotu ne domin neman hakkinsa kan rashin amincewa da ƴan takarar da ya mika wa INEC a madadin jam’iyyar.
A cikin takardar da TheCable ta gani, INEC ce wacce a ke ƙara ta ɗaya .
Ba a samu wakilcin hukumar zaben a gaban kotu ba a ranar 1 ga watan Nuwamba a lokacin da aka fara sauraren karar, haka kuma ba su gabatar da wata amsa ba.
A hukuncin da kotun ta yanke, ta umurci INEC “ta dora tare da nuna sunayen wadanda suka nemi takarar zaben 2023 wanda aka mika wa wanda ake kara a matsayin dan takararta na babban zaben da aka ce.