Home Labarai Kotu ta bayar da belin barawon tukunyar miya akan N10,000

Kotu ta bayar da belin barawon tukunyar miya akan N10,000

0
Kotu ta bayar da belin barawon tukunyar miya akan N10,000

Daga Hassan Y.A. Malik

Wani mutum mai shekaru 56 da aka bayyana sunansa da Tajuddeen Lateef ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke zamanta a Ikeja, jihar Legas, a jiya Alhamis bisa samunsa da laifin fasa shagon sayar da abinci tare da yin awon gaba da tunkuya makare da miyar dage-dage da aka ce darajarta ta kai N3,000, da wayar hannu ta N3,000 da kuma kudin cinikin mai shagon N10,000.

Kodayake dai Lateef ya ki amsa laifinsa, amma mai shigar da kara Sajan Mike Unah ya yi ikirarin cewa wanda ake karar ya aikata laifin a ranar 3 ga watan Mayu, a shago mai lamba 27 da ke kan titin Oko-Oba a unguwar Agege.
Sajan Mike ya ci gaba da cewa Lateef ya fasa shagon wata mata ne mai suna Tawa Amusa kuma wayar da ya sace ma ba tata bace ta wani ce da ake kira da Jami’u Onifade.

Sajan Mike ya ci gaba da cewa, wasu masu gadi ne da ke gadi a kusa da shagon suka kama shi.

Alkalin kotun, Majistare A.A. Fashola ya bayar da belin Lateef akan N10,000 tare da dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Mayu, 2018.

Mai shari’a dai ya bayyana cewa wannan laifi ya saba dokar laifuka sashe na 287 na kundin laifuka na jihar Legas 2011 kuma laifin na da hukunci daurin shekaru 3 a gidan kaso.