Home Labarai Kotu ta daure wanda yakai hari Masallaci a Landan shekaru 43

Kotu ta daure wanda yakai hari Masallaci a Landan shekaru 43

0
Kotu ta daure wanda yakai hari Masallaci a Landan shekaru 43
Police officers attend to the scene after a vehicle collided with pedestrians near a mosque in the Finsbury Park neighborhood of North London, Britain June 19, 2017. REUTERS/Neil Hall

Wani bature dan asalin kasar Burtaniya, ya tuka wata katuwar motardaukan kaya, ya nufi kan wasu mutane da suke Sallah a masallaci a birnin Landan, inda ya kashe mutum guda tare da jikkata wasu, a ranar 19 ga watan Yunin 2017.

Katu ta daure wannan mutum a gidan kurkuku daurin Shekaru 43 ko kuma daurin rai da rai a gidan kaso.

Shi dai wanda ya kai wannan hari, Darren Soborne dan shekaru 48 mazaunin Welsh Capital Cardiff, kotu ta same shi da aikata laifi, inda ya kashe mutum guda dan shekara 51 mai suna Makram Ali, sannan kuma yayi kokari kashe wasu a lokacin a Finsbury Park dake Arewacin Landan.

A lokacin da yake bayar da wannan hukunci, mai Shariah Bobbie Cheema-Grubb ta bayyanawa Osborne cewar, wannan abinda ya aikata ta’addanci ne, domin yayi nufin kashe rai.

Ta kara da cewar, shi ya nuna rashin tarbiyya are kuma da nuna wariya da nuna kyama ga wasu mutane.

“Kayi gangancin barin tunaninka maras kyau ya rudeka ka aikata aikin da ya janyo maka nadama”

Ruzina Akhtar ‘yar marigayin da aka kashe ta bayyanawa manema labarai a birnin landan cewar sun gamsu da wannan hukuncin da kotun ta yanke akan wanda ya kashe mahaifinta.

“Mahaifina mutumin kirki ne mai kaunar zaman lafiya, ba shi da wani abokin fada”

“Ba zamu taba iya jure tuna irin mawuyacin halin da ya shiga kafin mutuwarsa ba a dalilin wannan hari da aka kai masa aka raba shi da duniya”

Wasu rahotanni sunce, shi Osborne da ya kai wannan hari, ya samu damuwa ne tun bayan wani shirin talabijin da ya gani wanda aka bayyana matasan Musulmi masu yin jima’i barkatai, wanda wannan ne ya bata masa rai yayi nufin kaiwa Musulmi hari, a cewar wasu bayanai.

Sai dai kuma, Ofishin Firaministan Burtaniya, Theresa May ya gargadi al’ummar kasar akan kalaman da suke nuna wariya da kuma kyamatar juna, musamman a shafukan sada zumunta na intanet.

“Firaministan tace, ba daidai bane yadda kamfanoni a shafukan sadar da zumunta na intanet suke baiwa mutane damar maganganun na kyamatar juna da nuna wariya ga wasu jinsi na al’umma”