
Hassan Y.A. Malik
An yankewa wani ma’aikacin gwamnati, Ibrahim Lawal, mai shekaru 40 da haihuwa, hukunci daurin shekaru 2 a gidan maza bayan samunsa da kotu ta yi da laifin aikata lalata da wani yaro dan shekaru 17 da haihuwa.
Ibrahim Lawan, wanda ke zaune a Anguwar Fulani, cikin jihar Kaduna an zartar masa da wannan hukunci ne daga babbar kotun majistare da ke kan titin Daura, jihar Kaduna, a ranar Alhamis, bayan da kotun ta same shi da laifin aika rashin tarbiyya da fitsara.
Alkalin kotun, Mai shari’a Zainab Muhammad ta bashi zabin biyan tarar Naira dubu 20 ko kuma zaman gidan kaso na shekaru 2.
Mai gabatar da karar, furosukyuta Sunday Baba ya fadawa kotu cewa, wani Sunusi Idris da ke zama a unguwa daya da wanda ake karar ne ya kai rahoto ga ‘yan sanda a ranar 8 ga watan Janairu, 2018 cewa, wanda ake karar ya ja ra’ayin dansa mai shekaru 17 da haihuwa zuwa dakinsa, inda a can ne ya aikata lalata da shi.
An fara gurfanar da Ibrahim Lawal a gaban kuliya ne a ranar 12 ga watan Janairu, amma sai ya ki ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, har sai da kotu ta gabatar da shaidu har guda biyar da suka tabbatar da ya aikata laifin.
Furosikyuta ya ci gaba da cewa, ko da ‘yan sanda suka matsa da bincike, wanda ake zargi daga baya ya amsa cewar ya yi lalata da yaron sau da dama ta hanyar tursasawa.
Mai shari’a Zainab, yayin yanke hukuncinta ta bayyana cewa laifin ya sabawa sashe na 285 na kundin penal code ta jihar Kaduna ta shekarar 2017.
Ta kuma kara da cewa, wannan hukunci zai zama izina ga duk masu tunanin aikata irin wannan laifi a nan gaba.