
Daga Hassan Y.A. Malik
Maryam Sanda, wacce ke tsare a gidan maza tun bayan da aka zargeta da kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka ta samu beli.
Mai shari’a Yusuf Halilu na babbar kotun gwamnatin tarayya mai zamanta a Jabi, Abuja ne ya bada belin bayan da rahoton binciken lafiya ya bayyana cewa tana dauke da juna biyu.
Maryam ta fadawa kotu a ranar Litinin din da ta gabata cewa tana da bukata a bayar da belinta sakamakon halin da ta ke ciki na juna biyu.
In ba a manta ba dai, Maryam Sanda, ta bakin lauyanta, Joseph Daudu, a zaman kotun na baya ta roki kotu da ta tausaya mata ta bayar da belinta sakamakon juna biyu da ta ce tana dauke da shi.
Sai dai lauyan mai shigar da kara, James Idachaba ya kalubalanci rokon na Maryam, inda ya bayyana cewa ikirarin na Maryam tana da juna biyu har na watanni uku bashi da wata gamsasshiyar shaida.