Home Labarai Kotu ta soke zabubbukan fidda gwani na APC a jihar Ribas

Kotu ta soke zabubbukan fidda gwani na APC a jihar Ribas

0
Kotu ta soke zabubbukan fidda gwani na APC a jihar Ribas

Babbar kotun tarayya dake birnin Fatakwal a jihar Ribas ta rushe dukkan zabubbukan fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar Ribas da bangarorin jam’iyyar biyu suka yi.

Mai Shariah Kolawole Omitosho ya bukaci kada hukumar zabe ta kuskura ta yi amfani da ‘Yan takarar kowane sashe na bangarorin jam’iyyar da suka yi zabukan fidda gwani mabambanta.

An dai yi zabukan fidda gwani ne tsakanin bangaren tsohon Gwamnan jihar Ribas Rotimi Amaechi da na Magnus Abe, inda kotu tace dukkan zabukan biyu haramtattu ne.