Home Labarai Kotu ta umarci wata mace da ta maidawa mijinta sadakinsa

Kotu ta umarci wata mace da ta maidawa mijinta sadakinsa

0
Kotu ta umarci wata mace da ta maidawa mijinta sadakinsa

 Daga Hassan AbdulMalik

Wata kotun shari’ar musulunci ta biyu da ke garin Magajin Gari, jihar Kaduna ta umarci wata Maryam Muhammad da ta mayarwa da mijinta, Mansur Yakubu da sadakinsa na Naira dubu 20 sakamakon neman mijin nata ya sake da ta yi a gaban kotu.

Maryam ta bayyanawa kotu cewa ba za ta iya ci gaba da zama da mijinta ba, a saboda haka ne ta ke nema kotu da ta raba aurensu ta tsarin Khul’i.

“Ba zan iya ci gaba da zama da wannan mutumin ba, saboda haka na ke so kotu da ta raba aurenmu, zan mayar masa da sadakin da ya biya a lokacin aurena na Naira 20” a cewar Maryam.

Maryam ta roki kotu da ta tilasta Mansur Yakubu da ya dauki nauyin dan da suka haifa mai watanni biyu da haihuwa sannan kuma ya bari ta kwashe kayanta ba tare da tashin hankali ba.

Mansur, wanda ya shaidawa kotu cewa shi fa har yanzu yana kaunar matarsa ya ce, shi ba Naira dubu 20 ya biya sadaki ba, Naira dubu 25 ya mika aka aura masa Maryam.>

Mai Shari’a Musa Sa’ad ya bukaci da waliyan ma’auratan da su hallara a kotun, inda suka tabbatar da sadakin da Mansur ya bayar a matsayin Naira dubu 20.

Mai Shari’a ya bayyanawa kotu cewa mace na da damar da ta nemi saki ta sigar Khul’i, sannan ya umarci Maryam da ta biya Mansur sadakin Naira dubu 20 da ya biya kafin aura masa ita.

“Ni, Musa Sa’ad na warware auren Mansur Yakubu da Maryam Muhammad ta sigar Khul’i kamar yadda shari’ar addinin musulunci ta tanadar.”

Mai Shari’a Musa Sa’ad ya ci gaba da cewa, kotu ta yanke cewa Mansur zai dinga bawa Maryam Naira dubu 5 a kowane wata don kula da dansu.

Kotu ta umarci Maryam da ta debe kafatanin kayanta da ke gidan Mansur ta bar masa gidansa. Za ta kwashe kayan nata ne bisa sa idon ma’aikatan kotun.