
Daga Sani Bala Yauri
Babbar kotun tarayya dake zama a Wawa Cantonment a yankin Kainji dake jihar Neja a jiya Litinin ta yanke wa Haruna Yahaya mai shekaru 35 hukuncin shekaru sha biyar a gidan kaso bisa aikata laifin ta’addanci.
Wanda ake zargin yana daya daga cikin ‘yan Boko Haram din da suka sace ‘yan matan Chibok sama da 200 a jihar Borno a shekarar 2014.
Haruna ya amsa cewa yana daga cikin wadanda suka kai harin garuruwan Chibok a karanar hukumar Chibok da Gabsuri a karamar hukumar Damboa duk a jihar Borno