Home Labarai Kotu ta yankewa wani matashi hukuncin bulala 6 a Abuja

Kotu ta yankewa wani matashi hukuncin bulala 6 a Abuja

0
Kotu ta yankewa wani matashi hukuncin bulala 6 a Abuja

Hassan Y.A. Malik

Wata kotun yanki mai daraja ta 1 da ke zamanta a Karmo, Abuja, a jiya Alhamis, ta yankewa wani Yusuf Abdullahi hukuncin bulala 6 bisa zargin aikata barazana da rayuwar wata baiwar Allah.

Abdullahi, wanda ke zauna a tashar mota ta Jabi, Abuja, ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, inda ya roki alkalin kotun, Mai Shari’a Abubakar Sadiq da cewa kotu ta yi masa adalci musamman ma tunda bai wahalar da kotun ba.

Mai shari’a Abubakar Sadiq, bayan yanke hukuncin ya ja kunnen Abdullahi da cewa duk lokacin da aka kara kawo shi gaban kotun, to, fa, kotun ba za ta yi masa sassauci ba

Mai gabatar da kara. Florence Avhioboh, ta fadawa kotu cewa, wata Hafsat Dauda ce, da ke zaune a Jabi, Daki Biyu ce ta shigar da kokenta a ofishin ‘yan sanda na Utako, Abuja, a ranar 11 ga watan nan na Fabrairu.

Avhioboh ta tabbatar wa kotu cewa, bayan binciken da ‘yan sanda suka gudanar, sun samu wukar da Abdullahi ya fyalle tare da yin barazanar raunata Hafsat, kuma Abdullahi ya amsa laifinsa na cewa ya aikata laifinsa wanda ya ci karo da sashen dokar kundin penal code na 392.