Home Siyasa Kotu ta tabbatar da Sagagi a shugabancin PDP na Kano har zuwa Disambar 2024

Kotu ta tabbatar da Sagagi a shugabancin PDP na Kano har zuwa Disambar 2024

0
Kotu ta tabbatar da Sagagi a shugabancin PDP na Kano har zuwa Disambar 2024

 

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta fitar da wani umarni na dindindin da ya hana shelkwatar jam’iyyar PDP tsige shugaban jam’iyyar na Kano, Shehu Sagagi daga mukaminsa har zuwa ƙarshen wa’adin shugabancinsa a watan Disamba, 2024.

A ranar 14 ga watan Disamba, 2020 ne aka zaɓi shugabancin PDP a jihar, ƙarƙashin jagorancin Sagagi tare da sauran shuwagabannin jam’iyar a kananan hukumomi 44 na jihar Kano, inda kuma wa’adinsu na shekaru huɗu zai ƙare a ranar 13 ga Disamba, 2024.

Da yake yanke hukunci a yau Laraba, Mai Shari’a Taiwo Taiwo, ya ce Babban Kwamitin Jam’iyar, NWC ko kuma wani ɓangare mai iko a jam’iyyar, ba shi da ikon rusa shugabannin jam’iyar na jiha da aka zaɓa ta sahihiyar hanyar zaɓe.

Don haka ya bayar da umarni na dindindin da ke hani ga jam’iyyar rusa shugabancin jam’iyar na jiha da na kananan hukumomi har zuwa karshen wa’adinsu.

Ku tuna cewa a ranar 28 ga watan Afrilu ne kotun ta dawo da Sagagi da shugabannin jam’iyar a matakin kananan hukumomi 44 bayan da NWC ta sallame su.

Ana zargin dai Sagagi na tare da tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso.

A na zargin biyayyar da Sagagi ke yi wa shugaban na NNPP ne ya wargaza jam’iyyar a Kano, har ta kai ga ba ta da ƴan takarar Sanatan Kano ta Arewa da Kano ta Kudu da kuma kujeru da dama na ƴan majalisar jiha da na tarayya.