Home Kasuwanci Kotu ta umarci BUA da ya biya korarrun ma’aikatansa 11 kuɗaɗen sallama

Kotu ta umarci BUA da ya biya korarrun ma’aikatansa 11 kuɗaɗen sallama

0
Kotu ta umarci BUA da ya biya korarrun ma’aikatansa 11 kuɗaɗen sallama

 

Kotun Kasuwanci ta Ƙasa, NIC, ta umarci kamfanin fulawa na da ya biya ma’aikatansa 11 da ya kora kuɗaɗen sallamar su.

Da ya ke yanke hukuncin, mai Shari’a Ebeye Isele, ya bada umarnin da a biya masu ƙara su biyar da su ka haɗa da, Aliyu Kabara, Idris Isah, Abdullahi Mohammed, Mohammed Abdullahi da Ahmed Mohammed N1.4 million, N261,360, N216,000, N261,000 N522,720 a matsayin kuɗaɗen sallamar su.

Haka-zalika kotun ta umarci kamfanin da ya biya tafiyar sauran masu ƙara su shida, Rabiu Hamisu, Lawan Sanusi, Salisu Garba, Valentine Watsav, Yusuf Usman da Augustine Clement, albashi su na wata ɗaya bayan da su ka yi ƙasa da shekaru 5 su na aiki.

Kotun kuma ta ce dole ne a biya su cikin wata daya da yanke hukuncin.

Sai dai kuma kotun ta amince da sallamar ma’aikatan, inda ta ce bai saɓawa sharuɗɗa da ƙa’idojin ɗaukar su aiki ba.