Home Labarai Kotu ta umarci wata mata da ta bar gidan tsohon mijinta a cikin awa 72

Kotu ta umarci wata mata da ta bar gidan tsohon mijinta a cikin awa 72

0
Kotu ta umarci wata mata da ta bar gidan tsohon mijinta a cikin awa 72

 

A yau Laraba ne wata Kotun Shari’ar Muslunci da ke unguwar Magajin Gari a Jihar Kaduna ta umarci wata mata mai suna Rahma Usman da ta tattara kayan ta ta bar gidan tsohon mijin ta mai suna Abdulbasit Sulaiman cikin awanni 72.

Alƙalin kotun, Murtala Nasir, ya bada umarnin ne bayan da kotun ta tabbatar da cewa auren su ya mutu.

Alƙalin ya kuma umarci Sulaiman da ya riƙa baiwa tsohuwar matar ta sa Naira dubu 10 duk wata a matsayin kuɗin abinci har sai ta kammala iddar ta.

Tun a watan Nuwambar 2021 ne dai Sulaiman ya kai ƙarar tsohuwar mai ɗakin nasa, inda ya nemi kotu da ta kore ta da ga gidan tunda ta gama idda.

Ya kuma shaidawa kotun cewa tun 23 ga watan Disambar 2020 ya yi mata saki ɗaya.

Amma kuma lauyan wanda a ke ƙara, Sagir Hassan, ya ce Rahma ba ta gama iddar ta ba, sabo da haka za ta ci gaba da zama a gidan har sai ta kammala.

“Jinin haila biyu kawai ta yi, sabo da haka sai ta kammala iddar ta sannan za ta bar gidan,” in ji lauyan.

Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa a Muslunci, sai mace ta yi jinin haila uku sannan ne ta kammala iddar ta, har ma za ta iya wani auren.