
Wata Babbar Kotun Taraiya a Abuja ta wanke da kuma sakin tsohon Ministan Aiyuka na Musamman da Harkokin Gwamnati, Kabiru Turaki a kan zargin almundahanar kuɗaɗe.
Da ya ke ƙwarya-ƙwaryar hukunci a kan korafin da wanda a ke ƙara ya shigar na a dakatar da shari’ar, alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya ce Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC, ta gaza nuna laifin da Turaki da sauran waɗanda a ke zargi tare da shi su ka aikata kamar yadda hukumar ta ayyana a tuhume-tuhume 16 da ta shigar a cikin ƙarar.
A cewar Ekwo, waɗanda a ke ƙara sun kare kan su a kan shaidojin da shaidun masu ƙara su ka bayar a kotun a lokacin da ake tuhuma, inda ya ce shaidun sun dogara ne da “hujjojin son rai” da EFCC ta bayar.
Alkalin ya ce a lokacin da a ke tuhuma a kotun, an tabbatar da cewa Turaki ba shi ne wanda ya ke sanya hannu a asusun ma’aikatar ba, inda ya ƙara da cewa bai sahale a biya ko aika wasu kuɗaɗe ba.
Ya dogara ne da batun cewa Turaki ba mamba ba ne na kwamitin hada-hadar kuɗaɗe.
Ya kuma ce ba a samu wani fitar kuɗaɗe da ga ma’aikatar zuwa kamfanin Turaki ba.
Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawato cewa EFCC na tuhumar Turaki da sauran waɗanda a ke zargin da almundahanar kudade har Naira Miliyan 715.