Home Labarai Kotu ta yanke wa ɓarawon wayoyi wata 6 a gidan yari ko tarar N20,000 a Kano

Kotu ta yanke wa ɓarawon wayoyi wata 6 a gidan yari ko tarar N20,000 a Kano

0
Kotu ta yanke wa ɓarawon wayoyi wata 6 a gidan yari ko tarar N20,000 a Kano
Kotun Magistrate mai lamba 35 da ke zamanta a Nomansland, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Al-Mustapha Kofar-Mata ta yanke wa wani matashi, Nazifi Sunusi watanni 6 a gidan yari ko ya biya tarar naira dubu 20.
Tun da fari dai an gabatar da Sunusi,  ɗan kimanin shekaru 26, mazaunin Unguwar Dabai da ke Ƙaramar Hukumar Gwale bisa zarginsa da zuwa unguwar gobirawa cikin karamar hukumar Dala wanda ya haura gidan wani mutum ya sace wayoyinsu kirar Samsung da Techno, masu kimar kudi  kimanin Naira dubu ɗari da tara (N109,000.)
A zan kotun na yau Talata,  mai gabatar da ƙara a kotun, Rabi’atu Sule,  ta yi roƙo ga Mai Shari’a da ya yi umarnin karantawa wanda a ke tuhuma ƙunshin tuhume-tuhumen da a ke masa da yaren da zai fuskanta, inda  nan take kuwa alƙalin ya amince da hakan.
Nan take jami’in kotu ya fara karanta masa tuhumar da ake masa, inda ya ce masa “shin ko ka aikata wannan abubuwan da ake zargin ka dashi ?” sai kuwa wanda a ke zargin ya kada baki ya ce “ya mai shari’a babu wani ka a kan wannan batu, na aikata abinda ake zargin na akai.”
Bayan wannan iƙirarin ne sai mai gabatar da ƙara ta sake roƙom  kotu da tayi masa hukuncin na nan take.
Bayan gabatar da rokonne, sai alƙalin ya yankewa wannan matashi hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan gyaran hali sakamakon wadannan laifuka guda biyu, ko kuma zaɓin tara na Naira dubu 20.
Haka zalika mai alƙalin ya umarci Sunusi da ya biya waɗanda ya sacewa wayoyinsu kudinsu, wadanda kimar kudinsu yakai Naira dubu ɗari da  da tara (N109,000).
Sannan kuma ya hori mai lefin da ya zamanto mai ɗabi’u nagari a duk inda yasamu kansa.
Daga bisani Jami’in gidan gyaran hali, Mataimakin Sifeto Abbas Abubakar Musa ya tusa keyar Sunusi zuwa gidan yari har sai ya cika umarnin kotu.