Home Labarai Kotu ta yanke wa ɗan China hukuncin daurin shekara 5 a Kwara

Kotu ta yanke wa ɗan China hukuncin daurin shekara 5 a Kwara

0
Kotu ta yanke wa ɗan China hukuncin daurin shekara 5 a Kwara
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ilorin babban birnin jihar Kwara ta yanke wa wani dan China Gang Deng, hukuncin daurin shekara biyar saboda zargin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
A wani sako da hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce an gurfanar da dan Chinan mai shekara 29 kan zargin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, da mallakar ma’aidai masu yawa ba bisa ka’ida ba.
BBC ta rawaito cewa hukumar ta kama mista Gang a kauyen Tsagari, da ke karamar hukumar Edu a jihar a watan Satumba
Hukumar ta zarge shi da mallakar ma’adinai da nauyinsu ya kai ton 25, wadanda ake fitar da su zuwa kasar China domin yin baturan ababen hawa, da na wayar hannu, da na kyamarori, da kuma wasu na’urori masu amfani da wutar lantarki.