Home Labarai Kotu ta yanke hukunci kan matar da ta saci sa-hannun marigayi Abba Kyari

Kotu ta yanke hukunci kan matar da ta saci sa-hannun marigayi Abba Kyari

0
Kotu ta yanke hukunci kan matar da ta saci sa-hannun marigayi Abba Kyari

Wata babbar kotun Abuja da ke Gwagwalada ta samu wata Ramat Mercy Mba da laifin yin jabun sa hannun tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Marigayi Abba Kyari.

Sai dai mai shari’a Ibrahim Mohammad ya tanadi hukuncin da za a yanke mata zuwa ranar 16 ga watan Mayu.

Ya ba da umarnin a tsare matar, mai ƴaƴa biyar a gidan yari na Suleja.

Tunda fari, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ce ta gurfanar da Mba a watan Yunin 2022 kan tuhume-tuhume biyar da suka shafi zamba, damfara da yin sa hannu jabu, wanda ya saba wlda sashe na 13 na dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka na 200 da sashe na 320 (b), 366 na dokokin Penal Code Cap 89 na Arewacin Najeriya.