Home Labarai Kotu ta yanke wa likitan bogi hukuncin sharar titi da bulala 10 a Kano

Kotu ta yanke wa likitan bogi hukuncin sharar titi da bulala 10 a Kano

0
Kotu ta yanke wa likitan bogi hukuncin sharar titi da bulala 10 a Kano

 

 

Kotun Majistare mai lamba 47 a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Umar Ahmed hukuncin ɗaurin watanni 6, ko sharar titi ta tsawon makonni biyu da kuma bulala goma.

Tun da fari dai, kotun na tuhumar Ahmed da laifuka biyu da su ka haɗa da cuta da kuma yin sojan-gona.

A zaman kotun na jiya Alhamis, lauyar gwamnati, Asma’u Dalhatu Gwarzo, ta yi umarnin da kotun ta karanto wa wanda a ke zargi laifukan nasa.

Sai jami’in kotun, Auwal Yakubu Abdullahi ya karanto wa wanda a ke zargin laifukan sa, nan take kuma ya amsa.

Da ga ƙarshe, sai Mai Shari’a, Hadiza Muhammad Hassan, ta yanke masa hukuncin wata shida, ko sharar titi na sati biyu da kuma bulala 10.

Sannan kotun ta ce sai ya biya Naira dubu 14 ko daurin wata biyu, sakamakon samun sa da laifin karɓar kuɗin wani mara lafiya, bayan ya yi masa ƙaryar cewa shi ma’aikacin lafiya ne a asibitin Nassarawa.