Home Kanun Labarai Kotun Ɗaukaka-ƙara ta dawo wa da Sadiq Wali takararsa ta gwamnan Kano a PDP

Kotun Ɗaukaka-ƙara ta dawo wa da Sadiq Wali takararsa ta gwamnan Kano a PDP

0
Kotun Ɗaukaka-ƙara ta dawo wa da Sadiq Wali takararsa ta gwamnan Kano a PDP

A yau Juma’a ne kotun daukaka kara ta Kano ta mayar da Sadiq Wali a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Kano.

A ranar 22 ga watan Disamba, wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayyana Mohammad Abacha a matsayin zababben dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, tare da soke zaben fidda-gwani gwani da ya samar da Sadiq Wali a matsayin dan takara.

Sai dai a hukuncin da ya yanke, mai shari’a Usman Musale, kotun daukaka kara ta ce jam’iyyar PDP, reshen jihar ba ta da hurumin gudanar da zaben fidda gwani.

Kotun ta ci gaba da cewa Abacha ba shi da ikon kai Wali ƙara saboda bai shiga zaben fidda gwanin da ya fitar da Wali ɗin a matsayin ɗan takarar gwamna ba.