Home Labarai Kotun Duniya za ta yanke hukunci kan karar da Afirka ta Kudu ta shigar akan Isra’ila

Kotun Duniya za ta yanke hukunci kan karar da Afirka ta Kudu ta shigar akan Isra’ila

0
Kotun Duniya za ta yanke hukunci kan karar da Afirka ta Kudu ta shigar akan Isra’ila

A ranar Juma’a alƙalan Kotun Duniya (ICJ) za su yanke hukunci kan ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar da Isra’ila tana zarginta da aikata kisan ƙare-dangi a Gaza.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce cikin wata sanarwa da kotun ta fitar ranar Laraba, ta ce tawagar alƙalan 17 za su yanke hukunci kan ƙarar ranar Juma’a 26 ga watan Janairu da misalan ƙarfe 12:00 na rana agogon GMT.

A farkon wannan watan ne kotun ta saurari ƙarar cikin kwanaki biyu.

Afirka ta Kudu ta buƙaci kotun ta tilasta wa Isra’ila gaggauta dakatar da Isra’ila daga hare-haren da take yi wa yankunan Falasɗinawa.

Isra’ila ta musanta zargin da cewa an ”jirkita gaskiya”, sannan ta ce tana da damar kare kanta sannan mayaƙan Hamas take kai wa hare-hare ba fararen hula ba.

A hukuncin na ranar Juma’ar, kotun duniyar ba za ta duba ko Isra’ila ta aikata kisan ƙare-dangi ba.

A maimakon haka kotun za ta duba yiwuwar ɗaukar matakan gaggawa, da za su hana rikicin ci gaba da ƙazanta, a yayin da kotun za ta ci gaba da sauraron ƙara har na tsawon shekaru.

Idan kotun ta yanke hukuncin gaggauta dakatar da yaƙin, to ba dole ba ne Isra’ila ta yi biyayya ga hukuncin, wanda shi ne babban burin Afirka ta Kudu.

A ƙa’ida dole ne a yi biyyya ga hukuncin kotun, ba tare da ɗaukaka ƙara ba, to sai dai kotun ba ta da hurumin tilasta biyayya ga hukuncin da ta yi.

BBC Hausa