Home Siyasa Kotun Koli ta tabbatar da Laila Buhari a matsayin ƴar takarar Sanatan Kano-ta-Tsakiya a PDP

Kotun Koli ta tabbatar da Laila Buhari a matsayin ƴar takarar Sanatan Kano-ta-Tsakiya a PDP

0
Kotun Koli ta tabbatar da Laila Buhari a matsayin ƴar takarar Sanatan Kano-ta-Tsakiya a PDP

A yau Alhamis ne kotun koli ta tabbatar da zaben Laila Buhari a matsayin ƴar takarar Sanata ta jam’iyyar PDP a mazabar Kano-ta-Tsakiya.

Jam’iyyar PDP ta garzaya kotun koli, inda ta bukaci kotun kolin ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, sannan ta bayyana Damburam Nuhu a matsayin zababben dan takarar sanata a mazaɓar.

Amma a hukuncin da mai shari’a Mohammed Garba ya yanke, kwamitin mutum 5 da suka hada da Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, Ibrahim Saulawa, Adamu Jauro da Emmanuel Agim, ba su amince da dukkan dalilan daukaka karar ba.

Kwamitin ya kuma yi kakkausar suka tare da gargadin jam’iyyar PDP kan yin kama-karya.

A dalilansu na daukaka kara, lauyoyin PDP sun yi musun cewa alkalan kotun daukaka kara sun yi kuskure a shari’a kuma rashin adalci ne ƙarara lokacin da su ka yi amfani da tanadin sashe na 15 na dokar Kotun daukaka kara ta 2004 wajen yanke hukuncin Ms Buhari a kan cancantar ta, bayan sun sani sarai cewa ta gaza cika sharuddan da aka gindaya na tabbatar da sashen.

Jam’iyyar ta kuma ce alkalan kotun daukaka kara sun yi kuskure a shari’ar saboda rashin kula da tanadin sakin layi na 8 (i) na umarnin gudanar da ayyukan babbar kotun tarayya (Pre Election) na 2022, ta hanyar rike cewa babbar kotun tarayya, ta Kano na da hurumin sauraren karar da Mrs Buhari ta shigar.

PDP ta ci gaba da cewa alkalan kotun daukaka kara sun yi kuskure a lokacin da suka amince da daukaka karar tare da yin watsi da hukuncin da kotun ta yanke, gami da cewa mai shigar da kara a kotun daukaka kara ta tabbatar da cewa ita ce ‘yar takarar da ta dace a zaben Jam’iyyar PDP na fidda gwanin da ta gudanar domin zabar dan takararta na Sanatan Kano ta tsakiya.