Home Labarai Kotun majistre ta umarci matashi da ya share haraba bisa yunƙurin yin sata

Kotun majistre ta umarci matashi da ya share haraba bisa yunƙurin yin sata

0
Kotun majistre ta umarci matashi da ya share haraba bisa yunƙurin yin sata

 

A yau Juma’a ne wata Kotun Majistare da ke Ota a Jihar Ogun ta umarci wani matashi ɗan shekara 28, Abraham John, da ya share harabar kotun na tsawon kwana ɗaya bisa laifin haura gida da yunƙurin yin sata.

John, wanda ba a bayar da adireshinsa ba, ya amsa laifin karya wa, shiga da yunkurin yin sata.

Sai dai kuma ya roki kotu da ta yi masa sassauci.

Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun, Mai shari’a A.O.Adeyemi, ya yanke wa mai laifin hukuncin yi wa al’umma hidima na kwana ɗaya ba tare da zabin tara ba.

Tun da fari, Lauyan mai gabatar da kara, Sifeto E.O. Adaraloye, ya shaida wa kotun cewa John ya aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Yuli, da misalin karfe 11.40 a Ifelodun CDA, Ayetoro Itele, Ota.

Adaraloye ya shaida wa kotun cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya fasa gidan mai karar, gidan Popoola Kabiru da nufin yin sata.

Ya ce laifin ya saɓawa sashe na 412 na kundin laifuffuka, dokokin Ogun, 2006.