Home Labarai Kotun Ƙoli ta dakatar da hana amfani da tsofaffin kuɗaɗe

Kotun Ƙoli ta dakatar da hana amfani da tsofaffin kuɗaɗe

0
Kotun Ƙoli ta dakatar da hana amfani da tsofaffin kuɗaɗe

A yau Laraba ne Kotun Koli ta bada umarnin wucin-gadi da a dakatar da shirin janye tsofaffin daga hannun mutane daga watan Fabrairu.

Wani kwamiti mai mutane bakwai, karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro ne ya dakatar da matakin a wani hukunci da ya yanke a wata takardar bukatar da wasu jahohin Arewa guda uku da suka hada da Kaduna, Kogi da Zamfara suka gabatar.

Jihohi ukun dai sun gabatar da bukatar a ba su umarni na wucin-gadi na hana “gwamnatin tarayya, ta hannun babban bankin Najeriya, CBN, ko kuma bankunan kasuwanci dakatarwa ko tantancewa ko kuma kawo karshen wa’adin ranar 10 ga watan Fabreru na daina amfani da tsaoffin takardun Naira na 200, 500 da 1,000 har sai an saurare su da kuma yanke shawarar shawararsu kan sanarwar neman izinin shiga tsakani”.

Da ya ke yanke hukunci a kan kudirin, Okoro ya ce bayan an yi nazari sosai kan kudirin an ba da wannan bukata kamar yadda aka yi addu’a.

Don haka ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu domin sauraron manyan korafe-korafen.