Home Siyasa Kotun ƙoli ta tabbatar da Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar Sanata

Kotun ƙoli ta tabbatar da Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar Sanata

0
Kotun ƙoli ta tabbatar da Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar Sanata

Kotun koli ta bayyana shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a matsayin dan takarar sanata na jam’iyyar APC a Yobe.

Kotun kolin ta amince da daukaka karar da jam’iyyar APC ta shigar kan takarar Bashir Machina.

A hukuncin, uku daga cikin alkalai biyar sun amince da matsayar APC cewa bai kamata a fara karar a kotun ta hanyar sammaci na asali ba tunda ta kunshi zarge-zargen maguɗi.

A cewar kotun kolin, ginshikin karar ya nuna cewa ana tuhumar wadanda suka shigar da kara da maguɗi.