Home Siyasa Kotun Ƙoli ta tabbatar wa da Sanata Sani Hanga nasarar zaɓen sa

Kotun Ƙoli ta tabbatar wa da Sanata Sani Hanga nasarar zaɓen sa

0
Kotun Ƙoli ta tabbatar wa da Sanata Sani Hanga nasarar zaɓen sa

Kotun kolin Nijeriya, a yau Juma’a, ta tabbatar da dan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Sanata Rufa’i Sani Hanga a matsayin zababben Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya.

A wani hukunci da mai shari’a Uwani Abba Aji ta yanke, kotun kolin ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, inda ta umarci INEC ta amince da Sanata Hanga a matsayin dan takara.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ranar Litinin din da ta gabata ne aka ayyana tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar New Nigeria People Party (NNPP) duk da cewa ya fice daga jam’iyyar kafin zaben.

Sai dai bayan bayyana sakamakon zaben, wakilin jam’iyyar NNPP, Shehu Usman, ya ki amincewa da sunan Sanata Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaɓen .

Ya yi zargin cewa da gan-gan INEC ta ki sauya sunan Sanata Shekarau da dan takarar da jam’iyyar NNPP ta tsayar a zaben, Rufai Hanga.

Mista Usman ya yi ikirarin cewa akwai wani umarnin kotu da ya umurci hukumar zabe ta INEC da ta amince da sunan Sanata Hanga a matsayin wanda ya cancanta a zaben.

Sai dai kuma a yau hukuncin kotun kolin a yau ya warware dukka matsalar.