
Kotun koli ta yanke hukuncin cewa ɗalibai mata musulmi a jihar Legas za su iya sanya hijabi zuwa makaranta.
Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, wacce ta rubuta hukuncin mafi rinjaye, wanda mai shari’a Tijani Abubakar ya karanta, ta yi watsi da karar ne bisa hujjar cewa daukaka karar ba ta da wani dalili.
A wani mataki na hukuncin da kotun daukaka kara da ke Legas ta yanke a ranar 21 ga watan Yuli, 2016, wanda ya yi watsi da hukuncin da mai shari’a Grace Onyeabo ta babbar kotun ta ranar 17 ga Oktoba, 2014 na jihar Legas, wanda ya tabbatar da dokar hana hijabi.
A watan Oktoban 2014 ne babbar kotun Legas ta yanke hukuncin hana amfani da hijabi a makarantu, hukuncin da wata kotun daukaka kara ta soke a watan Yulin 2016.
A cikin yanke hukunci na bai daya, kotun daukaka kara ta lura cewa haramcin na nuna wariya ga daliban musulmi a jihar Legas.
A wani mataki na rashin gamsuwa da hukuncin kotun daukaka kara , gwamnatin jihar ta kai karar zuwa kotun koli.
Daga baya ta sanya dokar hana amfani da hijabi a watan Agustan 2018.