
A yau Alhamis ne wata kotun shari’ar Musulunci a Kano ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wani matashi dan shekara 28, Badamasi Abubakar, a gidan yari, bayan da ya amsa laifin yaye wa wata mata mayafi ba tare da izininta ba.
Abubakar, wanda ke zaune a unguwar Dan Marke Hotoro Quarters, Kano, ya amsa laifinsa na cin zarafi.
Alkalin kotun, Ismail Muhammed-Ahmed, ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 27 ga watan Yuli domin yanke masa hukunci.
Tun da fari, Lauyan masu shigar da kara, Sifeto Abdul Wada, ya shaida wa kotun cewa Summaiya Abdul ta Dan Marke Hotoro Quarters, ta kai karar ofishin ‘yan sanda na Hotoro a ranar 21 ga watan Yuni.
Mai gabatar da kara ya ce mai shigar da kara ta ce da misalin karfe 4 na yamma wanda ake karar ya ɗage mata mayafi ba tare da izininta ba, kuma da ta yi masa magana kawai sai ya kwaɗa mata mari.
Wada ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 165 da 166 na kundin laifuffuka.